(ABNA24.com) Shugaban kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Huthy ya ce, ko kadan basu tsoron yin gaba da gaba da sojojin Amurka, kuma sun so yin hakan da su amma su ka gudu.
A wani jawabi da ya gabatar a jiya Alhamis wanda tashar talabijin din ‘almasirah ta watsa, Sayyid Abdulmakil al-huthy ya kara da cewa; Amurka tana yaki da a’ummarmu ne ta fuskoki da dama da su ka hada tattalin arziki, soja, tsaro da kuma dukkanin bangarori.”
Jagoran na kungiyar Ansarullah ya kuma ce; Amurka ta gudu ta kasa fuskantarmu, amma sai ta turo ‘yan korenta, tana basu kariya da kuma makamai.
Al’ummar Yemen suna zargin Amurika da ingiza Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma ‘yan korensu a cikin kasar yemen domin su shelanta yaki akan kasar da al’ummarta.
/129
20 Yuni 2020 - 09:24
News ID: 1048233

Shugaban kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Huthy ya ce, ko kadan basu tsoron yin gaba da gaba da sojojin Amurka, kuma sun so yin hakan da su amma su ka gudu.